Kamfanin Dillancin Labaran Hauza: A farkon halittarsa, mutum yana kama da wani akwati fanko, amma a shirye yake ya samu tasiri a tsawon rayuwarsa daga al’adu da ɗabi’u, tunani da ƙimomi iri-iri, na gaskiya ko na ƙarya. Tsare-tsaren siyasa, tattalin arziki da zamantakewa ma suna taka rawa wajen samar da fahimtarsa da halayensa. Duk da haka, Allah Ya sanya wa mutum fitrar Allah da wata karkata na cikin zuciya zuwa sanin gaskiya da bin gaskiya, domin ya iya gane hanyar gaskiya a tsakanin tasirin muhalli daban-daban, ya kuma bi ta. Kamar yadda Allah Maɗaukaki Ya bayyana wannan gaskiya a cikin Alƙur’ani:
«فَأَقِمْ وَجْهَکَ لِلدِّینِ حَنِیفًا فِطْرَتَ اللَّهِ الَّتِی فَطَرَ النَّاسَ عَلَیْهَا لَا تَبْدِیلَ لِخَلْقِ اللَّهِ ذَٰلِکَ الدِّینُ الْقَیِّمُ وَلَٰکِنَّ أَکْثَرَ النَّاسِ لَا یَعْلَمُونَ.»
“Saboda haka, ka karkatar da fuskarka zuwa ga addini madaidaici. Wannan ita ce fitrar Allah wadda Ya halicci mutane a kanta. Babu sauyi ga halittar Allah. Wannan shi ne addini madaidaici, amma mafi yawan mutane ba su sani ba.” (Suratur Rum:30)
Wani lokaci sakaci da rashin sani suna mamaye mutum har ya manta da hakikanin fitrar Allah da ke cikin kansa, sannan da zaɓinsa da yardarsa ya nisanta daga tafarkin fitra da shiriya ta Allah. Sakamakon haka, maimakon ya sanya kiran cikin zuciyarsa na neman gaskiya ya zama fitilar da take jagorantar rayuwarsa, sai ya bi wata hanya dabam da hanyar fitrar Allah, sakamakon tasirin sha’awoyin rai da abubuwan da ke kewaye da shi.
Abin da yake ƙara muhimmantar da wannan batu shi ne cewa mantawa ko sauya tafarkin fitrar Allah na iya haifar da sauyin ni’imomin Allah.
Ku lura da wannan misali na Alƙur’ani: “Mutanen Ludu” mutane ne waɗanda aka azabtar saboda aikata manyan zunubai, daga cikinsu akwai Luwaɗi. Annabi Ludu (A.S) shi ne Manzon da aka aiko zuwa gare su. Bisa ga wasu majiyoyin tarihi, mutanen Ludu sun ci gaba da aikata manyan zunubai, ciki har da Luwaɗi, har daga ƙarshe suka fuskanci azabar Allah. Alƙur’ani Mai Girma ya bayyana azabar mutanen Ludu da kifar da garuruwansu da kuma saukar da duwatsu daga sama.
«وَأَمْطَرْنَا عَلَیْهِمْ مَطَرًا فَانْظُرْ کَیْفَ کَانَ عَاقِبَةُ الْمُجْرِمِینَ.»
“Mun saukar musu da ruwan sama (na duwatsu); ka duba yadda ƙarshen masu laifi ya kasance.” (Suratul A'araf: 84)
Haka kuma Ya ce:
«فَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا جَعَلْنَا عَالِیَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَیْهَا حِجَارَةً مِنْ سِجِّیلٍ مَنْضُودٍ.»
“Sa’ad da umarninMu ya zo, sai Muka mayar da samansu ƙasansu, kuma Muka saukar musu da duwatsu na yumɓu masu tauri, waɗanda aka jera ɗaya bayan ɗaya.” (Suratul Hud: 82)
Saboda haka, daga mahangar koyarwar ɗabi’a da addinin Musulunci, ɗaya daga cikin zunubai da zai iya nisantar da mutum daga tafarkin fitrar Allah, ya kuma zama sanadin sauyin ni’imomin Allah, shi ne “Luwaɗi”.
Zunubi da bijirewa tafarkin Allah suna fitar da ni’ima daga matsayin da aka nufa da ita, su mayar da “ruwan sama na rahama” zuwa “duwatsun azaba”. Wannan hoto yana kira ga mutum da ya yi tunani a kan sakamakon ruhaniya na zunubi, ya koma ga fitrar Allah, ya nemi gafara da rahamarSa.
Saboda haka, matsayin babban kalamin Amirul Muminina Ali (A.S) a cikin Du’ar Kumail yana ƙara bayyana:
«اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِیَ الذُّنُوبَ الَّتِی تُغَیِّرُ النِّعَمَ.»
“Ya Allah! Ka gafarta mini zunuban da suke sauya ni’imomi.”
Domin mumini ya kamata a koyaushe ya nemi gafara da rahamar Allah cikin ƙanƙan da kai, domin kawar da bala’i (kubuta daga illoli da sakamakon zunubi), da kuma tunkuɗe bala’i (kare kai daga faɗawa cikin zunubi da sauyin ni’imomi), tare da ɗaukar matakai wajen gyara kansa.
Amsa ga wata tambaya: Idan bisa ga koyarwar addini, zunubin Luwaɗi yana tattare da azabar Allah da sauyin ni’imomin Allah, to me ya sa masu aikata Luwaɗi a al’ummomin yau, musamman a ƙasashen Yamma, ba su fuskantar azabar Allah, kuma wasu ma suna morewa ni’imomin Allah?
Abin da ya kamata a fara lura da shi wajen amsa wannan tambaya shi ne cewa azabar da aka yi alkawari da ita ba ta takaita ga koyarwar Musulunci kaɗai ba.
A cikin Littafin Romawa na Injila an bayyana kamar haka: “Saboda haka Allah Ya bar su ga mugayen sha’awoyinsu masu kunyatarwa. Hatta matayensu sun musanya dangantakar halitta da wadda ba ta halitta ba. Haka ma maza sun bar dangantakar halitta da mata, suka ƙone da sha’awar juna. Namiji ya aikata abin kunya da namiji, suka samu a cikin kansu sakamakon da ya dace da karkacewarsu.” (Romawa 1:26–27)
Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da wani sakamako da ya dace da karkacewar Luwaɗi. To, wane irin sakamako ne wannan?
A cikin Littafin Firistoci (Leviticus) an ambaci wannan sakamako kamar haka: “Kada ka kwanta da namiji kamar yadda ake kwana da mace, domin abin ƙazanta ne... Kada ku ƙazantar da kanku da waɗannan abubuwa, domin al’umman da Zan kore su daga gabanku sun ƙazantu da waɗannan abubuwa. Ƙasar ta ƙazantu, saboda haka Zan hukunta ta saboda laifinta, ƙasar kuma za ta yi amai da mazaunanta. Saboda haka ku kiyaye farillai da dokokina...” (Leviticus 18:22, 24–26)
Fushin ƙasa da ɗaukar fansa a kanta, shi ne azabar da ake danganta ta da rashin kula da fitrar Allah da dabi’ar ɗan Adam; irin wannan azaba ce Alƙur’ani Mai Girma ma ya yi ishara da ita:
«فَلَمَّا جَاءَ أَمْرُنَا جَعَلْنَا عَالِیَهَا سَافِلَهَا...»
“Sa’ad da umarninMu ya zo, sai Muka mayar da samansu ƙasansu...”
Saboda haka, bisa ga wannan mahangar, azabar da aka yi alkawari da ita ba ta takaita ga koyarwar Musulunci kaɗai ba.
Wani muhimmin abu kuma da ya kamata a kula da shi wajen amsa wannan tambaya shi ne cewa jinkirin azabar Allah, da kuma samun ni’imomin Allah ba tare da an sauya su ba, ba hujja ba ce cewa Allah Ya amince da wannan aiki (= zunubi).
Allah Maɗaukaki Ya yi bayani a cikin Alƙur’ani game da mutanen da suka manta da umarnin Allah, amma a zahiri suna ci gaba da samun ni’imomin Allah:
«فَلَمَّا نَسُوا مَا ذُکِّرُوا بِهِ فَتَحْنَا عَلَیْهِمْ أَبْوَابَ کُلِّ شَیْءٍ حَتَّیٰ إِذَا فَرِحُوا بِمَا أُوتُوا أَخَذْنَاهُمْ بَغْتَةً فَإِذَا هُمْ مُبْلِسُونَ.»
“Sa’ad da suka manta da abin da aka tunasar da su da shi, sai Muka buɗe musu ƙofofin komai (na ni’imomi), har suka yi farin ciki da abin da aka ba su; sai kwatsam Muka kama su, a lokacin kuma sai suka zama masu yanke ƙauna.” (Suratul An'an:44
Saboda haka ne Manzon Allah (S.A.W.A) ya ce:
«إِذَا رَأَیْتَ اَللَّهَ یُعْطِی عَلَی اَلْمَعَاصِی فَإِنَّ ذَلِکَ اِسْتِدْرَاجٌ مِنْهُ.»
“Idan ka ga duniya tana tafiya daidai ga masu aikata zunubi, to wannan istidraj ne daga Allah, wato barin su su ci gaba a hankali har zuwa halaka.” (Tafsir Nur al-Thaqalayn, juzu’i na 1, shafi na 718)
Saboda haka, bisa ga koyarwar addini, “sunnah ta istidraj” tana daga cikin dokoki da hanyoyin Allah. Ma’anarta ita ce, idan mutum ya nisanta kansa daga tafarkin fitrar Allah, amma a lokaci guda yana ci gaba da more ni’imomin Allah, ya kamata ya sani cewa yana kan hanyar halaka. Kuma wannan jin daɗi da rashin azaba na ɗan lokaci ba ya zama alamar rahamar Allah ga mai zunubi.
Muhimmancin wannan batu ya kai matsayin da Amirul Muminina Ali (A.S) ya gargaɗe mu da cewa:
«یَا ابْنَ آدَمَ، إِذَا رَأَیْتَ رَبَّکَ سُبْحَانَهُ یُتَابِعُ عَلَیْکَ نِعَمَهُ وَ أَنْتَ تَعْصِیهِ، فَاحْذَرْهُ.»
“Ya ɗan Adam! Idan ka ga Ubangijinka Mai Tsarki yana ci gaba da zubo maka ni’imominsa, alhali kana saɓa masa, to ka yi hattara da Shi (kada azabarsa mai tsanani ta kasance tana jiran ka).” (Nahjul-Balagha, Hikima ta 25)
Ko da yake akwai bayanai masu yawa game da haɗarin zunubin Luwaɗi da hujjojin da ake gabatarwa wajen tunasar da mutane wannan haɗari, amma domin taƙaitawa, za mu tsaya a nan.
Mustafa Amini
Ra'ayinka